18 'Yan yara sukan raina ni su yi mini dariya sa'ad da suka gan ni.
18 Har ’yan yara suna rena ni; in sun gan ni sai su fara yi mini riyar reni.
Daga nan Elisha ya haura zuwa Betel. A hanya sai ga waɗansu samari sun fito daga cikin gari, suna yi masa eho, suna cewa, “Ka bar wurin nan, kai mai saiƙo.”
A hannun dama 'yan tā da zaune tsaye sun taso mini, Sun runtume ni, sun tura ni a hanyarsu ta hallakarwa.
“Amma yanzu waɗanda na girme su, sai ba'a suke mini, Waɗanda iyayensu maza ba su fi karnukan da suke kiwon garken tumakina ba.
Za a yi ta cutar juna. Matasa ba za su girmama manyansu ba, talakawa ba za su girmama na gaba da su ba.
Har matata ma ba ta iya jurewa da ɗoyin numfashina, 'Yan'uwana maza kuwa ba su ko zuwa kusa da ni.
Aminaina na kusa sukan dube ni, duban ƙyama, Waɗanda na fi ƙaunarsu duka sun zama maƙiyana.
A shirye kuke ku sari 'yan'uwanku, Ku sa musu laifi.