16 Sa'ad da na kira barana, ba ya amsawa, Ko a lokacin da na roƙe shi ya taimake ni.
16 Na kira bawana, amma bai amsa ba, ko da yake na roƙe shi da bakina.
sai hadiri ya taso daga hamada, ya rushe gidan, ya kashe 'ya'yanka duka, ni kaɗai na tsira na zo in faɗa maka.”
Waɗanda sukan ziyarce gidana sun manta da ni. Barorina mata na gidana sun maishe ni kamar baƙo daga wata ƙasa.
Har matata ma ba ta iya jurewa da ɗoyin numfashina, 'Yan'uwana maza kuwa ba su ko zuwa kusa da ni.