Na ji mutane da yawa suna sa mini laƙabi cewa, ‘Razana ta kowace fuska,’ Suna cewa, ‘Mu la'anta shi! Mu la'anta shi!’ Har ma da abokaina shaƙiƙai Suna jira su ga fāɗuwata. Suka ce, ‘Watakila a ruɗe shi, Sa'an nan ma iya rinjayarsa Mu ɗauki fansa a kansa.’
Da dare tana kuka mai zafi, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf a kumatunta. Dukan masoyanta ba wanda yake ta'azantar da ita. Dukan abokanta sun ci amanarta, sun zama maƙiyanta.
Sa'an nan dukan 'yan'uwan Ayuba mata da maza da dukan waɗanda suka san shi a dā, suka zo gidansa suka ci abinci tare da shi, suka yi juyayin abin da ya same shi, suka ta'azantar da shi, saboda dukan wahalar da Ubangiji ya aukar masa. Kowannensu ya ba shi 'yan kuɗi da zoben zinariya.