Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayuba 19:13 - Littafi Mai Tsarki

13 “'Yan'uwana sun yashe ni, Na zama baƙo ga idon sanina.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 “Ya raba ni da ’yan’uwana maza; abokaina sun zama baƙi gare ni.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayuba 19:13
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka sa abokaina su yashe ni, Ka sa sun ware ni. An kange ni, ba yadda zan kuɓuta.


Ka sa har abokaina na kusa sun yashe ni, Duhu ne kaɗai abokin zamana.


Kamar baƙo nake ga 'yan'uwana, Haka ma ga iyalina, kamar baƙo nake.


Magabtana duka suna mini ba'a, Maƙwabtana sun raina ni, Waɗanda suka san ni kuwa suna jin tsorona, Sa'ad da suka gan ni a kan titi sukan guje mini.


A lokacin da na ba da hanzarina na farko, ba wanda ya goyi bayana, sai duk suka yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba.


Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.


Zuciyata ta karai saboda cin mutuncin da ake ci mini, Ni kuwa ba ni da mataimaki, Na sa zuciya za a kula da ni, Amma babu. Na sa zuciya zan sami ta'aziyya, Amma ban samu ba.


Abokaina da maƙwabtana ba su ko zuwa kusa da ni, saboda miyakuna, Har iyalina ma sun guje mini.


Ka gajiyar da ni, ya Allah, Ka shafe iyalina.


Ina so Allah ya ga hawayena, Ya kuma ji addu'ata.


Sa'an nan dukan 'yan'uwan Ayuba mata da maza da dukan waɗanda suka san shi a dā, suka zo gidansa suka ci abinci tare da shi, suka yi juyayin abin da ya same shi, suka ta'azantar da shi, saboda dukan wahalar da Ubangiji ya aukar masa. Kowannensu ya ba shi 'yan kuɗi da zoben zinariya.


Har da shaƙiƙin abokina, Wanda na fi amincewa da shi. Wanda muke ci tare, ya juya yana gāba da ni.


Da dare tana kuka mai zafi, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf a kumatunta. Dukan masoyanta ba wanda yake ta'azantar da ita. Dukan abokanta sun ci amanarta, sun zama maƙiyanta.


“Na kira masoyana, amma suka yaudare ni, Firistocina da dattawana a cikin birni sun hallaka Saboda neman abincin da za su ci su rayu.


Amma ku abokaina, kun ruɗe ni, Kamar rafi wanda yakan ƙafe da rani.


Amma sa zuciyarsu ta ƙare a gefen busassun rafuffuka,


Duk an manta da ni kamar matacce, Na zama kamar abin da aka jefar.


Masu son kashe ni, sun haƙa mini tarkuna, Masu so su cuce ni, suna barazanar lalatar da ni, Yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.


Ƙaunar da nake da ita ta yin ibada a Haikalinka Tana iza ni a ciki kamar wuta, Zargin da suke yi a kanka, ya fāɗa a kaina.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ