Ubangiji ya zama kamar maƙiyi, ya hallaka Isra'ila. Ya hallaka fādodinta duka, Ya mai da kagaranta kango. Ya aukar wa Yahuza da makoki da baƙin ciki mai yawa.
Ya ja bakansa kamar abokan gāba, Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi. Ya hallaka dukan abin da yake da bansha'awa. A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta.