Sai Absalom da dukan mutanen Isra'ila suka ce, “Shawarar Hushai Ba'arkite ta fi ta Ahitofel kyau.” Haka Ubangiji ya nufa ya wofintar da kyakkyawar shawarar Ahitofel don ya jawo wa Absalom masifa.
Aka faɗa wa Dawuda cewa, “Ahitofel yana cikin 'yan maƙarƙashiya tare da Absalom.” Sai Dawuda ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka wofintar da shawarar Ahitofel.”
Zuciyar Sarkin Suriya kuwa ta ɓaci ƙwarai a kan wannan al'amari, don haka ya kirawo fādawansa, ya ce musu, “Wane ne wannan da yake cikinmu, yana goyon bayan Sarkin Isra'ila?”