5 “Za a kashe hasken mugun mutum, Harshen wutarsa ba zai ƙara ci ba.
5 “An kashe fitilar mugu; harshen wutarsa ya daina ci.
Adalai suna kama da haske mai haskakawa ƙwarai, mugaye kuwa suna kamar fitilar da take mutuwa.
Gama mugun mutum ba shi da sa zuciya, ba abin da zai sa zuciya a kansa nan gaba.
Idan ka zagi iyayenka, za ka mutu kamar fitilar da ta mutu cikin duhu.
“An taɓa kashe hasken mugun mutum? Ko masifa ta taɓa fāɗa wa wani daga cikinsu? Allah ya taɓa hukunta wa mugu da fushi,
Dukanku da kuke ƙulle-ƙullen hallaka juna Ƙulle-ƙullenku za su hallaka ku! Ubangiji kansa zai sa wannan ya faru, Za ku gamu da mummunar ƙaddara.
Hanyar mugaye kuwa duhu ne baƙi ƙirin, kamar duhun dare. Sukan fāɗi, amma ba su san abin da ya sa suka yi tuntuɓe ba.
Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.
Cutar kanka kake yi saboda fushin da kake ji. Duniya za ta ƙare ne sabili da kai? Za a kawar da duwatsu sabili da kai?
Amma mugaye suna kama da tumbatsar teku, gama ba ta iya natsuwa. Ruwanta kuma yana tumbatsa, ya gurɓace, ya ƙazantu.”
Sa'ad da na shafe ka, zan rufe sammai, In sa taurarinsu su duhunta, Zan sa girgije ya rufe rana, Wata kuma ba zai haskaka ba.
Ba kuwa zai kuɓuta daga duhu ba. Zai zama kamar itacen da wuta ta ƙone rassansa, Kamar itace kuma da iska ta kaɗe furensa.
Girmankai da fāriya suke bi da mugaye, wannan kuwa zunubi ne.