Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu kai da kawowa, waɗanda aka tanada wa matsanancin duhu har abada.
Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hankali irin na dabba. Ya tafi ya zauna tare da jakunan jeji, yana ta cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.
Nan take sai abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar ya tabbata. Aka kore shi daga cikin mutane. Ya shiga cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar gashin gaggafa, akaifunsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.
Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasar da ta fi girma. A can za ka mutu a kusa da karusan da kake fāriya da su. Abin kunya kake a gidan maigidanka!