“Duba rana tana zuwa, sa'ad da dukan masu girmankai, da mugaye za su ƙone kamar tattaka, a ran nan za su ƙone ƙurmus ba abin da zai ragu, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
“Amma ga shi, saboda ku na hallakar da Amoriyawa, Dogayen mutanen nan masu kama da itatuwan al'ul, Ƙarfafa kuma kamar itatuwan oak, Na hallaka su ƙaƙaf.
Don haka, kamar yadda tattaka da busasshiyar ciyawa sukan yanƙwane su ƙone a wuta, saiwoyinku za su ruɓe, furanninku kuma za su bushe. Iska za ta kwashe su, domin kun ƙi abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya koya muku.