10 An binne masa tarko a ƙasa, An kafa masa tarko a hanyarsa.
10 An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa; an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.
Dawuda kuma ya ce, “Da ma shagalinsu ya zama musu tarko, abin shammatarsu, Sanadin faɗuwarsu kuma, har aniyarsu ta koma kansu.
Zan yarɓa masa ragata in kama shi. Zan kai shi Babila, wato ƙasar Kaldiyawa, duk da haka ba zai gan ta ba, ko da yake zai rasu a can.
Yakan aukar da garwashin wuta Da kibritu mai cin wuta a kan mugaye, Yakan hukunta su da harshen wuta mai ƙuna.
Tarko ya kama diddigensa ya riƙe shi,
“Kewaye da shi duka razana tana jiransa, Duk inda ya nufa tana biye da shi,