2 Na lura da yadda mutane suke yi mini mummunar ba'a.
2 Ba shakka masu yi mini ba’a suna kewaye da ni; idanuna suna ganin tsokanar da suke yi mini.
Ina so Allah ya ga hawayena, Ya kuma ji addu'ata.
Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu, Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi, Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu'o'ina.
Duk wanda ya je wurin Maɗaukaki Zai zauna lafiya, Duk wanda yake zaune a inuwar Mai Iko Dukka,
Kullayaumi za su arzuta, 'Ya'yansu kuma za su zauna lafiya a ƙasar.
Ku ba ni zarafi in yi magana, sa'an nan in na gama ku amsa in kun ga dama.
Da Allah ya bincike ku sosai, Zai iske wani abin kirki ne a cikinku? Kuna tsammani za ku ruɗi Allah, kamar yadda kuke ruɗin mutane?
Ayuba, kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba? Kana tsammani maganganunka na ba'a Za su sa mu rasa abin da za mu mayar maka?
Yanzu kuwa sun mai da wannan karin magana a kaina. Da mutane suka ji, Suka zo suka yi ta tofa mini yau a fuska.
Ga shi kuwa, dukanku kun gani da kanku, Me ya sa kuka zama wawaye?