22 Yanzu shekaruna wucewa suke yi, Ina bin hanyar da ba a komawa.”
22 “Shekaru kaɗan suka rage in kama hanyar da ba a komawa.
Amma ɗan mutum ya mutu, ƙarshensa ke nan, Ya mutu, a ina yake a lokacin nan?
Idan mutum ya mutu, zai sāke rayuwa kuma? Amma zan jira lokaci mafi kyau, In jira sai lokacin wahala ya wuce.
Tsawon kwanakin ransa, an ƙayyade su tun can, An ƙayyade yawan watannin da zai yi, Ka riga ka yanke haka ya Allah, ba su sākuwa.
Sa'an nan za ka ji tsoron hawan tudu, tafiya kuma za ta yi maka wuya. Gashin kanka zai furfurce. Za ka ja jikinka. Ba sauran sha'awar mace. Daga nan sai kabari, masu makoki kuwa su yi ta kai da kawowa a kan tituna.
Da a ce na mutu a lokacin, da yanzu ina huce,
An jima kaɗan zan tafi, ba kuwa zan komo ba faufau, Zan tafi ƙasa mai duhu, inda ba haske,
“Ina so wanda zai yi roƙo ga Allah domina, Kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.
“Ƙarshen raina ya gabato, da ƙyar nake numfashi, Ba abin da ya rage mini sai kabari.