16 Na yi ta kuka har fuskata ta zama ja wur, Idanuna kuma suka yi luhuluhu.
16 Fuskata ta yi ja don kuka idanuna sun kukumbura;
Sai ya ce musu, “Raina na shan wahala matuƙa, har ma kamar na mutu. Ku dakata nan, ku zauna a faɗake.”
“Ina kuka saboda waɗannan abubuwa, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf daga idanuna. Gama mai ta'azantar da ni, Wanda zai sa in murmure yana nesa da ni. 'Ya'yana sun lalace, Gama maƙiyi ya yi nasara!”
Mutane da yawa suka gigice sa'ad da suka gan shi, Ya munana har ya fita kamannin mutum.
Toka ce abincina, Hawayena kuwa sun gauraya da abin shana,
Na gaji da kira, ina neman taimako, Maƙogwarona yana yi mini ciwo, Idanuna duka sun gaji, Saboda ina zuba ido ga taimakonka.
Sa'ad da ban hurta zunubaina ba, Na gajiyar da kaina da yawan kuka dukan yini.
Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, Gama ina shan wahala, Idanuna sun gaji saboda yawan kuka, Na kuwa tafke ƙwarai!
Baƙin cikina ya kusa makantar da ni, Hannuwana da ƙafafuna sun rame, sun zama kamar kyauro.
Mutuwa ta ɗaure ni da igiyarta tam, Razanar kabari ta auka mini, Na cika da tsoro da alhini.
Ina so Allah ya ga hawayena, Ya kuma ji addu'ata.
Gama tsananin duhu kamar safiya yake gare su, Sun saba da razanar duhu.