Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayuba 15:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ko ka taɓa jin shirye-shiryen da Allah ya yi? Ko kai kaɗai kake da hikima a cikin mutane?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Kana sauraron shawarar Allah? Ko kana gani kai kaɗai ne mai hikima?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayuba 15:8
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji? Ko kuwa wa ya taɓa ba shi wata shawara?”


Irmiya ya ce, “Gama wane ne a cikin annabawan nan ya taɓa neman shawarar Ubangiji don ya fahimci maganarsa, ko kuwa wane ne ya taɓa kasa kunne don ya ji maganarsa?


“Wa ya taɓa sanin tunanin Ubangiji, har da zai koya masa?” Mu kuwa tunaninmu na Almasihu ne.


Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana.


Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa, “Zan yi magana da misalai, Zan sanar da abin da yake ɓoye tun farkon duniya.”


Ya amsa musu ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Sama, amma su ba a ba su ba.


A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.


Hakika Ubangiji ba yakan aikata kome ba, Sai da sanin bayinsa annabawa.


gama Ubangiji yana ƙin mutanen da suke aikata mugunta, amma yakan rungumi adalai ya amince da su.


Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, Yakan koya musu alkawarinsa.


Kwanakin da nake gaɓar raina, Lokacin da ni'imar Allah take kan gidana,


“Aha! Ashe, kai ne muryar jama'a, Idan ka mutu hikima ta mutu ke nan tare da kai.


Da ya faɗa maka hikima tana da fannoni da yawa. Akwai abubuwa waɗanda suka fi ƙarfin ganewar ɗan adam. Duba, Allah ya ƙyale wani ɓangare na laifinka.


“Sanin gaibu na Ubangiji Allahnmu ne, amma abubuwan da aka bayyana namu ne, mu da 'ya'yanmu har abada, don mu kiyaye dukan maganar dokokin nan.”


Zurfin hikimar Allah da na saninsa da rashin iyaka suke! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincikewa, hanyoyinsa kuma sun fi gaban bin diddigi!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ