4 Kana karya jama'a, kana hana su jin tsoron Allah, Kana hana su yin addu'a gare shi.
4 Amma ka ma rena Allah ka hana a yi addu’a gare shi.
Wato mun soke Shari'a ke nan ta bangaskiyar nan? A'a, ko kusa! Sai tabbatar da ita muka yi.
Ba na tozarta alherin Allah. Don da ta wurin bin Shari'a ake samun adalcin Allah, ashe, da Almasihu ya mutu a banza ke nan.”
Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a, kada kuma su karai.
Da kuma waɗanda suka juya, suka bar bin Ubangiji, Waɗanda ba su neman Ubangiji, ba su kuma roƙonsa.”
Sa'ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga ko wane ne da yake ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?” Sai a amsa, “A'a.” Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.”
Ba su yi kuka gare ni da zuciya ɗaya ba, Sa'ad da suke kuka a gadajensu, Sun tsattsaga jikinsu domin abinci da ruwan inabi. Sun yi mini tawaye.
Ya Ubangiji, lokaci ya yi da za ka yi wani abu, Saboda mutane sun ƙi yin biyayya da dokarka!
Ko Mai Iko Dukka zai zama abin farin ciki a gare shi? Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?
“A cikin irin wannan wahala Ina bukatar amintattun abokai, Ko da na rabu da Allah, ko ina tare da shi.
“In da ni ne kai, da sai in juya wurin Allah, In kai ƙarata a wurinsa.
Ba wani mai hikima wanda zai yi magana irin taka, Ko kuma ya kāre kansa da irin maganganun da ba su da ma'ana.
Mugun lamirinka shi ne yake magana yanzu, Kana ƙoƙari ka ɓuya a bayan maganganunka na wayo.