17 “Yanzu ka saurara, ya Ayuba, ga abin da na sani.
17 “Ka saurare ni, zan kuma yi maka bayani; bari in gaya maka abin da na gani,
“Ka yi mini haƙuri kaɗan, ni kuwa zan nuna maka, Gama har yanzu ina da abin da zan faɗa in kāre Allah.
“Ku mutane masu hikima, ku ji maganata, Ku kasa kunne ga abin da zan faɗa, ku masana.
“Amma yanzu, kai Ayuba, ka yarda ka ji maganata, Ka kasa kunne ga dukan abin da zan faɗa.
Kai, Ayuba, mun koyi wannan don mun daɗe muna nazari, Gaskiya ce, don haka ka yarda da wannan.”
Mutum yakan sha mugunta kamar yadda yake shan ruwa, Hakika mutum ya lalace, ya zama mai rainako.
Mutane masu hikima sun koya mini gaskiya Wadda suka koya daga wurin kakanninsu, Ba su kuwa ɓoye mini asirin kome ba.
Duk abin da ka hurta, na taɓa jinsa, Na gane da shi sarai. Iyakar abin da kuka sani, ni ma na sani. Ba ku fi ni da kome ba.