Bayan da Ubangiji ya gama faɗa wa Ayuba waɗannan magana, sai ya ce wa Elifaz, mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokan nan naka biyu, gama ba ku faɗi gaskiya game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.
Sa'ad da uku daga cikin abokan Ayuba, wato Elifaz daga birnin Teman, da Bildad daga ƙasar Shuwa, da Zofar daga ƙasar Na'ama, suka ji labarin irin yawan wahalar da Ayuba yake sha, sai suka kama hanya suka tafi su ziyarce shi, su ta'azantar da shi.
Sai Elifaz mutumin Teman, da Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na'ama suka tafi suka yi kamar yadda Ubangiji ya faɗa musu, Ubangiji kuwa ya karɓi addu'ar Ayuba.