Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.
Amma a bar kututturen da saiwoyinsa a ƙasa Ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. A bar shi can cikin ɗanyar ciyawar saura, Ya jiƙe da raɓa, Ya yi ta cin ciyawa tare da namomin jeji.
Ko da mutum ɗaya cikin goma zai ragu a ƙasar, shi ma za a hallaka shi. Zai zama kamar kututturen itacen oak wanda aka sare.” Wato kututturen alama ce ta tohuwar jama'ar Allah zuwa gaba.
Yana da ganyaye masu kyau Da 'ya'ya jingim don kowa da kowa ya ci. Namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa, Tsuntsayen sama kuma suka zauna a rassansa. Dukan masu rai a gare shi suka sami abinci.