2 Sukan yi girma su bushe nan da nan kamar furanni, Sukan shuɗe kamar inuwa.
2 Yana tasowa kamar fure yana kuma shuɗewa; kamar inuwa, ba ya daɗewa.
Domin “Duk ɗan adam kamar ciyawa yake, Duk darajarsa kamar furen ciyawa take, Ciyawar takan bushe, furen yakan kaɗe,
Kwanakinmu 'yan kaɗan ne kawai, Ba mu san kome ba, Mu inuwa ne kawai a fuskar duniya.
Alhali kuwa ba ku san abin da gobe za ta kawo ba. Wane iri ne ranku? Ai, kamar hazo yake, jim kaɗan sai ya ɓace.
Gama mu kamar baƙi ne, masu yawo a gabanka kamar kakanninmu. Kwanakinmu a duniya kamar inuwa ne, ba za mu tsere wa mutuwa ba.
Shi kamar hucin iska yake, Kwanakinsa kuwa kamar inuwa mai wucewa ne.
Raina kamar inuwar maraice yake, Kamar busasshiyar ciyawa nake.
Ga mugaye ba zai tafi daidai ba, kamar inuwa ransu yake. Za su yi mutuwar ƙuruciya domin ba su da tsoron Allah.
Adalai za su yi yabanya Kamar itatuwan giginya, Za su yi girma kamar itatuwan al'ul na Lebanon.
Shi ne mai yiwuwa ne mugu ya yi girma kamar tsire-tsire, Masu aikata mugayen ayyuka kuma su arzuta, Duk da haka za a hallaka su ɗungum.
Mai yiwuwa ne mutum yana raye da safe Amma ya mutu ba a sani ba kafin maraice.
Zai ama kamar itacen inabi Wanda 'ya'yansa suka kakkaɓe tun kafin su nuna, Kamar itacen zaitun wanda bai taɓa yin 'ya'ya ba.
Za su shuɗe kamar busasshiyar ciyawa, Za su mutu kamar yadda tsire-tsire suke bushewa.
“Ga shi, ka gajerta yawan kwanakina! Yawan kwanakina a wurinka kamar ba kome ba ne. Hakika duk mutum mai rai, Bai fi shaƙar iska ba.
“A kan me zan sa zuciya, ya Ubangiji? A gare ka nake dogara.
Ina nishi da ƙarfi, Ba abin da ya ragu gare ni, In banda ƙashi da fata.
Amma kai, ya Ubangiji, sarki ne kai har abada, Dukan zamanai masu zuwa za su tuna da kai.