Yakubu ya ce wa Fir'auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.”
“Hakika ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya bayyana da ya fi Yahaya Maibaftisma girma. Duk da haka, wanda ya fi ƙanƙanta a Mulkin Sama ya fi shi.
Saboda haka rai ba wani abu ba ne a gare ni, domin dukan abin da yake cikinsa bai kawo mini kome ba sai wahala. Duka banza ne, ba abin da nake yi sai harbin iska kawai.
Ga Adamu kuwa ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga 'ya'yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tun da ka aikata wannan za a la'antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka.