5 Kada ku faɗi kome, Wani sai ya ce kuna da hikima!
5 In da za ku yi shiru gaba ɗaya! Zai zama muku hikima.
Banda haka ma, ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, mai basira.
“Ku yi shiru ku ba ni zarafi in yi magana. Duk abin da zai faru, ya faru.
Ya 'yan'uwana ƙaunatattu, ku san wannan, wato, kowa yă yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi,
Yawan damuwarka yana iya sa ka yi mafarkai. Yawan maganarka kuma yana iya sa ka ka yi maganar wauta.
Ashe, ba abin mamaki ba ne, Da masu hankali suka kame bakinsu A waɗannan kwanaki na mugunta.
Mutanen nan uku sun daina ba Ayuba amsa, saboda yana ganin kansa adali ne.
“Me ya sa kuke azabta ni da maganganu?
“Ayuba, mutane kamarka sun taɓa yin shiru? Da ka yi ƙoƙari ka kasa kunne da mun yi magana da kai.
Ka dinga yin magana ke nan har abada? A kullum maganarka ita ce dahir?
Ayuba, kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba? Kana tsammani maganganunka na ba'a Za su sa mu rasa abin da za mu mayar maka?
“Ku saurara mini, zan faɗi ƙarata.
Ku dube ni, ashe, wannan bai isa ya sa ku yi zuru, Ku firgita, ku yi shiru ba?
Ni kuma sai in tsaya don ba su ce kome ba? Sun tsaya kurum, don ba su da ta cewa?