Sa'ad da na ga ba ku cece ni ba, sai na yi kasai da raina, na haye don in yi karo da Ammonawa. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuna. Me ya sa kuka zo yau don ku yi yaƙi da ni?”
Ya yi kasai da ransa har ya kashe Bafilisten, Ubangiji kuwa ya ba Isra'ilawa babbar nasara. Kai ma ka gani, ka kuwa yi murna. Me ya sa za ka ɗauki alhakin Dawuda, wanda bai yi maka laifin kome ba?”
Zan sa masu zaluntarku su karkashe juna, Za su yi māye, da kisankai, da fushi. Sa'an nan dukan 'yan adam za su sani, ni ne Ubangiji, Wanda ya cece ku, ya fanshe ku. Za su sani ni ne Allah Mai Iko Dukka na Isra'ila.”