10 Ko da yake kun ɓoye son zuciyarku, Duk da haka zai tsauta muku,
10 Ba shakka zai kwaɓe ku in kun nuna sonkai a ɓoye.
Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan, Shari'a kuma ta same ku da laifin keta umarni.
Tilas ku daina yin rashin gaskiya a shari'a, Ku daina goyon bayan mugaye!
Son zuciya kuke yi, ko ba haka ba? Kuna goyon bayan Allah? Za ku goyi bayan Allah sa'ad da aka gurfanar da ni gaban shari'a?
Ba zan yi wa kowa son zuciya ba, Ko kuma in yi wa wani fādanci.
Ba ya nuna sonkai ga sarakuna, Ko kuma ya fi kulawa da attajira fiye da matalauta, Gama shi ya halicce su duka.
Yanzu fa ku yi tsoron Ubangiji. Ku lura da abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu bai yarda da rashin yin adalci ba, ko son zuciya, ko karɓar rashawa.”