Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayuba 12:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ba ka shan wahalar kome, duk da haka ka maishe ni abin dariya. Ka bugi mutumin da yake gab da fāɗuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Mutanen da ba su da damuwa suna jin daɗin ganin waɗanda suke dab da fāɗuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayuba 12:5
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai wawayen nan suka ce wa masu hikimar, ‘Ku sa mana ɗan manku kaɗan mana, fitilunmu na mutuwa!’


Adalai suna kama da haske mai haskakawa ƙwarai, mugaye kuwa suna kamar fitilar da take mutuwa.


Ina tafiya a kan tafarkinka kullum, Ban kuwa kauce ba.


Zan kuma ce wa raina, “Lalle ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagali.” ’


Ku girmama Ubangiji Allahnku, Kafin ya kawo duhu, Kafin kuma ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan dutse, da duhu duhu, Sa'ad da kuke neman haske, sai ya maishe shi duhu, Ya maishe shi duhu baƙi ƙirin.


Idan ka zagi iyayenka, za ka mutu kamar fitilar da ta mutu cikin duhu.


Na ce, “Ina kan fāɗuwa,” Amma, ya Ubangiji, madawwamiyar ƙaunarka ta riƙe ni.


“Za a kashe hasken mugun mutum, Harshen wutarsa ba zai ƙara ci ba.


In da a ce a matsayina kake, ni kuma ina a naka, Ina iya faɗar duk abin da kake faɗa yanzu. Da sai in kaɗa kaina da hikima, In dulmuyar da kai a cikin rigyawar maganganu.


“Idan jaki ya sami ciyawar ci, muradinsa ya biya, In ka ji saniya ta yi shiru, tana cin ingirici ne.


Sakayya da ɗaukar fansa nawa ne, A lokacin ƙafarsu za ta zame, Gama ranar masifarsu ta kusa, Hallakarsu za ta zo da sauri.’


Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu, Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi, Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu'o'ina.


Amma ɓarayi da marasa tsoron Allah suna zaune cikin salama, Ko da yake ƙarfinsu ne kaɗai allahnsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ