Duniya kanta za ta yi tangaɗi kamar mashayi, ta yi ta yin lau kamar rumfa a lokacin hadiri. Nauyin zunuban duniya ya rinjaye ta har ƙasa, za ta fāɗi, ba za ta ƙara tashi ba.
Ubangiji ne ya sa su ba da gurguwar shawara. Sakamakon haka sai Masar ta yi ta aikata dukan abu a hugunce, tana tangaɗi kamar bugagge wanda santsi na kwasarsa cikin aman da ya yi.
To, ga shi, hannun Ubangiji na kanka, za ka makance, ba za ka ga rana ba har wani lokaci.” A nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi, ya yi ta neman wanda zai yi masa jagora.
Muna ta lalubar bango kamar makafi, muna ta lalubawa kamar marasa idanu. Da tsakar rana muke ta tuntuɓe, sai ka ce da almuru. A tsakanin waɗanda suke da cikakken ƙarfi, kamar matattu muke.
Da tsakar rana za ku riƙa lalubawa kamar makaho, ba za ku yi arziki cikin ayyukanku ba. Za a riƙa zaluntarku, ana yi muku ƙwace kullum, ba wanda zai cece ku.