Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.
Ubangiji ne ya yi taurarin Kaza da 'ya'yanta Da mai farauta da kare. Ya mai da duhu haske, Rana kuwa dare. Shi ya kirawo ruwan teku ya bayyana, Ya shimfiɗa shi a bisa ƙasa. Sunansa Ubangiji ne.
Ɗaya daga cikin fādawan ya ce, “A'a, ranka ya daɗe, sarki, ai, annabi Elisha ne wanda yake cikin Isra'ila, yake faɗa wa Sarkin Isra'ila maganar da kake faɗa a ɗakin kwananka.”