Wata rana ya je yana sujada a gidan gunkinsa Nisrok, sai biyu daga cikin 'ya'yansa, Adrammelek da Sharezer, suka kashe shi da takubansu, sa'an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Wani daga cikin sauran 'ya'yansa, wato Esar-haddon, ya gāje shi ya zama sarki.
Ubangiji Mai Runduna ne ya shirya wannan! Ya shirya haka ne don ya kawo ƙarshen girmankanta saboda abin da suka aikata, don ya ƙasƙantar da manyan mutanenta.
‘Hakika, kamar yadda jiya na ga jinin Nabot da na 'ya'yansa, ni Ubangiji, zan sāka maka saboda wannan gona.’ Yanzu sai ka ɗauke shi, ka jefar da shi a wannan gona kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”
Sairus shi ne zaɓaɓɓen sarki na Ubangiji! Ubangiji ya sa shi ya ci al'ummai, Ya aike shi ya tuɓe ikon sarakuna, Ubangiji zai buɗe masa ƙofofin birni. Ubangiji ya ce wa Sairus,