Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, Ɗan Ragon kuwa zai cinye su, shi da waɗanda suke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, amintattu, domin shi ne Ubangijin iyayengiji.”
Sairus shi ne zaɓaɓɓen sarki na Ubangiji! Ubangiji ya sa shi ya ci al'ummai, Ya aike shi ya tuɓe ikon sarakuna, Ubangiji zai buɗe masa ƙofofin birni. Ubangiji ya ce wa Sairus,
Da suka kawo sarakunan a wurin Joshuwa, sai Joshuwa ya kirawo dukan Isra'ilawa, sa'an nan ya ce wa shugabannin mayaƙa, waɗanda suka tafi tare da shi, “Ku matso kusa, ku taka wuyan sarakunan nan.” Suka kuwa zo kusa, suka taka wuyansu.