Ayuba 12:10 - Littafi Mai Tsarki10 Allah shi ne yake bi da rayukan talikansa. Numfashin dukan mutane kuwa a ikonsa yake. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Ran kowace halitta yana a hannunsa, haka kuma numfashin dukan ’yan adam. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.