Shi ya sa wa kowane abu lokacinsa. Shi ne kuma ya sa mana buri mu san abin da yake nan gaba, amma fa bai ba mu cikakken sanin ayyukan da yake yi ba, tun daga farko har zuwa ƙarshe.
Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba? Ubangiji Madawwamin Allah ne? Ya halicci dukkan duniya. Bai taɓa jin gajiya ko kasala ba. Ba wanda ya taɓa fahimtar tunaninsa.
Wa ya taɓa hawa cikin Sama ya sauko? Wa ya taɓa kama iska cikin tafin hannunsa? Wa ya taɓa ƙunshe ruwa cikin rigarsa? Wa kuma ya kafa iyakar duniya? Ina sunansa, ina kuma sunan ɗansa? Hakika ka sani!