Bayan da Ubangiji ya gama faɗa wa Ayuba waɗannan magana, sai ya ce wa Elifaz, mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokan nan naka biyu, gama ba ku faɗi gaskiya game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.
“Da a ce ina da wanda zai kasa kunne gare ni, Da sai in sa hannu a kan abin da na faɗa, Allah kuwa Mai Iko Dukka ya amsa mini. “Da ƙarar da maƙiyana suke kai ni, a rubuce ne,