Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa, Ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji, Gama kana tare da ni! Sandanka na makiyayi da kerenka Suna kiyaye lafiyata.
Dukanmu mutuwa za mu yi, kamar ruwan da ya zube a ƙasa, wanda ba ya kwasuwa, haka za mu zama. Allah ba yakan ɗauke rai kurum ba, amma yakan shirya hanya domin wanda ya shuɗe ba zai ɓata daga gabansa ba.
Ba su kula da ni ba, Ko da yake na cece su daga ƙasar Masar. Na bi da su a cikin hamada, A ƙasa mai tuddai da kwazazzabai, Busasshiya mai yawan hatsari, Ba a bi ta cikinta, Ba wanda yake zama cikinta kuma.
Idan mutum ya rayu har shekaru da yawa, bari ya yi murna a cikinsu duka. Sai dai kuma ya tuna da kwanakin duhu, gama sun fi yawa. Duk abin da ya faru banza ne.