2 Kada ka hukunta ni, ya Allah. Ka faɗa mini laifin da kake tuhumata da shi.
2 Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni, amma ka gaya mini laifin da na yi maka.
Ni bawanka, kada ka gabatar da ni a gaban shari'a, Gama ba wanda ba shi da laifi a gare ka.
Tun da yake Allah ya ɗauka, ni mai laifi ne, To, me zai sa in damu?
Saboda haka a yanzu, ba sauran kayarwa ga waɗanda suke na Almasihu Yesu.
Amma ya Ubangiji, Allahna, ka taimake ni, Yadda ka alkawarta, Ka cece ni sabili da alherin ƙaunarka.
Ka gafarta zunubaina da kurakuraina masu yawa na ƙuruciyata. Saboda madawwamiyar ƙaunarka da alherinka, Ka tuna da ni, ya Ubangiji!
Ta ƙaƙa za ka iya jayayya da shi? Yana yiwuwa ya yi maka tambayoyi guda dubu Waɗanda ba wanda zai iya ba da amsarsu.
“Mai neman sa wa wani laifi ya jā da Mai Iko Dukka? Wanda yake gardama da Allah, bari ya ba da amsa.”
Ko na yi zunubi ina ruwanka, Kai mai ɗaure mutane? Me ya sa ka maishe ni abin bārata? Ni wani babban kaya mai nauyi ne a gare ka?
Kuskure da laifi guda nawa na yi? Waɗanne irin laifofi ake tuhumata da su?
“Ba da 'yan adam nake faɗa ba, Ina da isasshen hanzarin da zai sa in yi fushi.
Me ya sa kake yi wa Allah gunaguni, Cewa ba ya karɓar maganarka ko ɗaya?
Ka ji ni, ya Ubangiji, sa'ad da na ya yi kira gare ka! Ka yi mini jinƙai ka amsa mini!