Ba za ka iya gafarta mini zunubina ba? Ba za ka kawar da kai ga muguntar da na aikata ba? Ba da daɗewa ba zan rasu in koma a ƙura, Lokacin da ka neme ni ba za ka same ni ba.”
‘Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, kana gafarta mugunta da laifi, amma ba za ka ƙyale mai laifi ba, gama kakan ɗora wa 'ya'ya alhakin muguntar iyaye, har tsara ta uku da ta huɗu.’
Ni ne mai nuna ƙauna ga dubbai, mai gafarta mugunta, da laifi, da zunubi, wanda ba zai kuɓutar da mai mugunta ba, amma saboda laifin iyaye nakan hukunta 'ya'ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu.”