Iliya ya yi tafiyarsa yini guda cikin jeji, ya tafi ya zauna a gindin wani itace ya yi roƙo domin ya mutu, yana cewa, “Yanzu ya isa haka, ya Ubangiji, ka karɓi raina, gama ban fi kakannina ba.”
A sa'ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro. Yunusa ya ji kamar zai suma saboda zafin rana da take bugun kansa. Sai ya so ya mutu, ya ce, “Gara in mutu da ina zaune da rai.”