Ayuba 1:5 - Littafi Mai Tsarki5 A kowane lokacin da aka gama da liyafar, Ayuba yakan tashi da sassafe, kashegarin liyafar, yă miƙa hadayu don yă tsarkake 'ya'yansa. Haka yake yi kullum, don yana zaton mai yiwuwa ne ɗaya daga cikin 'ya'yan ya yi zunubi, ya saɓi Allah a ɓoye. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20205 Bayan lokacin bikin ya wuce, sai Ayuba yă aika su zo don yă tsarkake su. Tun da sassafe zai miƙa hadaya ta ƙonawa domin kowannensu, don yana tunani cewa, “Mai yiwuwa ’ya’yana sun yi wa Allah zunubi, ko sun la’anta shi a cikin zuciyarsu.” Haka Ayuba ya saba yi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |