Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Amos 9:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Ko da za su nutsa zuwa lahira, Zan kama su. Ko sun hau Sama, Zan turo su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Ko da sun tona rami kamar zurfin kabari, daga can hannuna zai fitar da su. Ko da sun hau can sama daga can zan sauko da su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Amos 9:2
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ko da Babila za ta hau samaniya, Ta gina kagara mai ƙarfi a can, Duk da haka zan aiki masu hallakarwa a kanta, Ni Ubangiji na faɗa.”


Ko da yake kina shawagi can sama kamar gaggafa, Gidanki kuma yana can cikin taurari, Daga can zan saukar da ke,” in ji Ubangiji.


Sai ya ce musu, “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walƙiya.


Tsoronki da ake ji da girmankanki sun ruɗe ki, Ke da kike zaune a kogon dutse, a kan tsauni, Ko da yake kin yi gidanki can sama kamar gaggafa, Duk da haka zan komar da ke ƙasa, Ni Ubangiji na faɗa.”


Mutane za su ɓuya a kogwannin duwatsu, ko su haƙa ramummuka a ƙasa, suna ƙoƙarin tserewa daga fushin Ubangiji, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa, sa'ad da ya zo domin ya girgiza duniya.


Lahira tsirara take a gaban Allah, Haka kuma Halaka take a gaban Allah.


Mai yiwuwa ne ya ƙasaita, ya zama kamar hasumiya a sararin sama. Ya ƙasaita har kansa ya taɓa gizagizai.


Ba wani duhu, ko duhu baƙi ƙirin Inda masu aikata mugunta za su ɓuya.


sa'an nan zan tura ki tare da waɗanda suke gangarawa zuwa lahira, zuwa wurin mutanen dā. Zan sa ki zauna a ƙarƙashin ƙasa inda ya zama kufai, tare da waɗanda suke gangarawa zuwa lahira, don kada a zauna a cikinki, amma zan ƙawata ƙasar masu rai.


An yi wannan domin kada itatuwan da suke bakin ruwa su yi girma, su yi tsayi da yawa har kawunansu su kai cikin gizagizai, domin kuma kada itacen da yake shan ruwa ya yi tsayi kamarsa, gama an bashe su ga mutuwa zuwa lahira, tare da 'yan adam masu gangarawa zuwa cikin kabari.”


Duk da haka ka ce, ‘Allah bai san kome ba. Gizagizai sun lulluɓe shi, ƙaƙa zai iya yi mana shari'a?’


Ya yiwu Allah ya bar shi ya yi zamansa lafiya, Amma a kowane lokaci zai sa ido a kansa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ