Amos 8:5 - Littafi Mai Tsarki5 Kuna ce wa kanku, “Mun ƙosa keɓaɓɓun kwanakin nan su wuce, Mu sami damar yin kasuwancinmu. Yaushe Asabar ɗin za ta ƙare ne? Ko mā sami damar kai hatsinmu kasuwa, Mu sayar musu da tsada, Mu yi awo da ma'aunin zalunci, Mu daidaita ma'auni yadda za mu cuci mai saya? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20205 Kuna cewa, “Yaushe Sabon Wata zai wuce don mu sayar da hatsi, Asabbaci ta wuce, don mu sayar da alkama?” Mu yi awo da ma’aunin zalunci mu ƙara kuɗin kaya mu kuma cutar da mai saya, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji ya ce, “Idan kun juyo kuna kiyaye ranar Asabar, kuka daina annashuwarku a tsattsarkar ranata, kuka kuma kira Asabar ranar murna, tsattsarkar rana ta Ubangiji, mai daraja, idan kun girmama ta, har kuka daina bin son zuciyarku, ba ku kuma bar shagulgula su ɗauke hankalinku ba, ko ku hurta maganganun banza,