Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Amos 8:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Mutane za su raunana, su riƙa kai da kawowa, Daga gabas zuwa yamma, daga kuma kudu zuwa arewa. Za su dudduba ko'ina suna neman saƙo daga Ubangiji, Ba kuwa za su samu ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Mutane za su yi ta tangaɗi daga teku zuwa teku suna yawo daga arewa zuwa kudu, suna neman maganar Ubangiji, amma ba za su samu ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Amos 8:12
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wanda ba nawa ba ne, gāba yake da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.


“Amma kai, Daniyel, sai ka rufe maganar, ka kuma kulle littafin, har zuwa ƙarshen lokaci. Mutane da yawa za su yi ta kai da kawowa, ilimi kuma zai ƙaru.”


Mutum mai fāriya ba zai taɓa zama mai hikima ba sam, amma mutum mai basira yakan koya a sawwaƙe.


Sa'ad da kuke miƙa hadaya, kuna miƙa 'ya'yanku hadaya ta ƙonawa, kuna ƙazantar da kanku ta wurin gumakanku har wa yau, to, za ku iya tambayata, ya ku mutanen Isra'ila? Ni Ubangiji Allah ba na tambayuwa gare ku.


“Ɗan mutum, ka faɗa wa dattawan Isra'ila cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na ce kun zo ku yi roƙo a wurina, amma hakika, ba na roƙuwa a gare ku.’


Yaron nan Sama'ila yana yi wa Ubangiji aiki a hannun Eli. A lokacin nan Ubangiji bai cika yin magana da mutane ba, ba safai kuma ake samun wahayi ba.


Inda ba a bin faɗar Allah, jama'a za su kangare, amma mai farin ciki ne wanda yake kiyaye dokar Allah.


Sa'an nan za ku kira gare ni, amma ba za ku same ni ba. Za ku neme ni a ko'ina, amma ba za ku same ni ba.


Da garkunan tumaki da na awaki, da na shanunsu Za su tafi neman Ubangiji, Amma ba za su same shi ba, Gama ya rabu da su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ