Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Amos 7:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Ubangiji kuwa ya dakatar da nufinsa, ya ce, “Wannan ma ba zai faru ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa. “Wannan ma ba zai faru ba,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Amos 7:6
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ashe, dā ma can ban faɗa ba, kafin in bar gida, cewa irin abin da za ka yi ke nan? Ai, dalilin da ya sa na yi iyakar ƙoƙarina in gudu zuwa Tarshish ke nan. Na sani kai mai taushin hali ne, mai jinƙai, mai haƙuri. Kai kullum mai alheri ne, a shirye kake kuma ka dakatar da nufinka na yin hukunci.


Allah kuwa ya ga abin da suka yi, ya ga yadda suka bar mugayen ayyukansu, sai ya dakatar da nufinsa, bai hallaka su ba.


Ubangiji kuwa ya dakatar da nufinsa, Ya ce, “Abin da ka gani, ba zai faru ba.”


Ashe, Hezekiya Sarkin Yahuza da dukan Yahuza sun kashe shi ne? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji, ya roƙi alherinsa ba? Ashe, Ubangiji bai janye masifar da ya hurta a kansu ba? Yanzu fa gab muke da mu jawo wa kanmu babbar masifa.”


Ubangiji zai ji juyayin mutanensa, Zai 'yantar da bayinsa.


Ya Ubangiji, sai yaushe za ka ji tausayinmu? Ka ji tausayin bayinka!


Sa'an nan suka zubar da gumakan da suke wurinsu, suka yi wa Ubangiji sujada. Shi kuwa ya damu saboda azabar da Isra'ilawa suke sha.


Sa'ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan taimake shi, ya kuwa cece su daga abokan gāba dukan kwanakin mahukuncin. Gama Ubangiji ya ji ƙansu saboda nishinsu, da zaluncin da ake yi musu.


Sai Ubangiji ya ce, “Zan shafe mutum daga duniya, mutum da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, gama na damu da na halicce su.”


Saboda su ne ya tuna da alkawarinsa, Ya sāke ra'ayinsa saboda ƙaunarsa mai yawa.


‘Idan za ku zauna a ƙasan nan, to, zan gina ku, ba zan rushe ku ba. Zan dasa ku, ba zan tumɓuke ku ba, gama zan janye masifar da na aukar muku.


Ku kyakkece zuciyarku, ba tufafinku kaɗai ba.” Ku komo wurin Ubangiji Allahnku. Gama shi mai alheri ne, mai jinƙai, Mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, Yakan tsai da hukunci.


Ubangiji kuma ya nuna mini wani wahayi. A wahayin sai na gan shi, yana tsaye kusa da bangon da ake ginawa. Yana riƙe da igiyar awon gini.


Ubangiji kuwa ya huce, ya janye niyyarsa ta jawo masifa a kan jama'arsa.


Allah ya aiko mala'ikansa don ya hallaka Urushalima, amma sa'ad da yake gab da hallaka ta, sai Ubangiji ya gani, ya janye shirin annobar, ya ce wa mala'ikan hallakarwa, “Ya isa, janye hannunka.” Mala'ikan Ubangiji kuwa na tsaye kusa da masussukar Arauna Bayebuse.


Amma Allah ya yi wa jama'arsa jinƙai, Ya gafarta zunubansu, Bai hallaka su ba. Sau da yawa yakan kanne fushinsa, Ya dakatar da hasalarsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ