Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Amos 7:2 - Littafi Mai Tsarki

2 A wahayin, na ga fara ta cinye kowane ɗanyen ganye a ƙasar. Sai na ce, “Ka gafarta wa jama'arka, ya Ubangiji! Ƙaƙa za su tsira? Ga su 'yan kima ne, marasa ƙarfi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Sa’ad da suka cinye kome, sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ka gafarta! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Amos 7:2
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benaiya, ya rasu. Sai na faɗi rubda ciki na fashe da kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah, za ka ƙare sauran mutanen Isra'ila ƙaƙaf ne?”


Sarkin Assuriya ya aiko babban shugaban mayaƙansa don ya zagi Allah mai rai. Da ma Ubangiji Allahnka ya ji waɗannan zage-zage ya kuma hukunta waɗanda suka yi su. Don haka sai ka yi addu'a ga Allah saboda mutanenmu waɗanda suka ragu.”


Sa'ad da suke karkashewar, aka bar ni, ni kaɗai, sai na faɗi rubda ciki, na yi kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah za ka hallaka dukan sauran Isra'ilawa saboda zafin fushinka a kan Urushalima?”


suka ce wa annabi Irmiya, “Muna roƙonka, ka roƙi Ubangiji Allahnka dominmu, dukanmu da muka ragu, gama mu kima muka ragu daga cikin masu yawa, kamar yadda kake ganinmu da idonka.


Irmiya ya ce, “Ko da yake zunubanmu su ne shaidunmu, Ya Ubangiji, ka yi taimako saboda sunanka! Gama kāsawarmu ta yi yawa, Domin mun yi maka zunubi.


Ta rufe dukan fuskar ƙasa har ƙasar ta yi duhu. Ta cinye kowane tsiro na ƙasar da dukan 'ya'yan itatuwa waɗanda ƙanƙara ta rage. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar.


Aka kuwa hana su cutar ciyayin duniya, ko tsiro, ko kowane itace, sai dai mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu.


Gama wane ne ya taɓa raina ranar ƙananan abubuwa? Amma za su yi murna da ganin igiyar awo a hannun Zarubabel. Waɗannan fitilu bakwai su ne alama Ubangiji yana kai da kawowa a duniya.”


Sa'an nan na ce, “Ya Ubangiji, in nufinka ne ka bari! Ƙaƙa jama'arka za su tsira? Ga su 'yan kima ne, marasa ƙarfi.”


Ya Ubangiji, ka ji mu. Ya Ubangiji, ka garfarce mu. Ya Ubangiji, ka saurare mu, ka yi wani abu saboda sunanka. Ya Allahna, kada ka yi jinkiri domin da sunanka ake kiran birninka da jama'arka.”


Masifa riɓi biyu ta auko miki, Yaƙi ya lalatar da ƙasarki, Mutanenki suka tagayyara da yunwa.


Ka cece ni, ya Ubangiji, Ba sauran mutanen kirki, Ba kuma za a sami amintattun mutane ba.


Ya ce, “Idan na sami tagomashi a gare ka, ya Ubangiji, ina roƙonka, ka yi tafiya tare da mu, ko da yake jama'a masu taurinkai ne, ka gafarta laifinmu, da zunubinmu, ka sa mu zama abin gādonka.”


Sai firistoci masu hidimar Ubangiji, Su yi kuka a tsakanin shirayi da bagade, Su ce, “Ya Ubangiji, ka ceci jama'arka, Kada ka bar gādonka ya zama abin zargi Da abin ba'a a tsakiyar al'ummai. Don kada al'ummai su ce, ‘Ina Allahnsu?’ ”


“Na sa darɓa, da domana Su lalatar da amfanin gonakinku. Fāra kuma ta cinye lambunanku Da gonakin inabinku, da itatuwan ɓaurenku, Da na zaitun ɗinku. Duk da haka ba ku komo wurina ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ