Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Amos 7:17 - Littafi Mai Tsarki

17 to, ga abin da Ubangiji ya ce maka, ya kai Amaziya, ‘Matarka za ta zama karuwa a birni, za a karkashe 'ya'yanka a cikin yaƙi. Za a rarraba wa waɗansu ƙasarka, kai kanka kuwa za ka mutu a ƙasar arna. Za a sa jama'ar Isra'ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 “Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “ ‘Matarka za tă zama karuwa a cikin birni, kuma da takobi za a kashe ’ya’yanka maza da mata. Za a auna ƙasarka a kuma raba ta, kai kuma za ka mutu a ƙasar arna. Ba shakka Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Amos 7:17
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba za su zauna a ƙasar Ubangiji ba, Amma mutanen Ifraimu za su koma Masar. Za su ci haramtaccen abinci a Assuriya.


A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, Sarkin Assuriya ya ci Samariya, ya kwashe Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.


Ubangiji ya ce, “Haka jama'ar Isra'ila za su ci ƙazantaccen abincinsu a cikin sauran al'umma inda za a kai su bautar talala.”


Saboda haka, in ji Ubangiji, ‘Zan kawar da kai daga duniya. Za ka mutu a wannan shekara domin ka kuta tayarwa ga Ubangiji.’ ”


Abin da ya faɗa ke nan, ‘Za a kashe Yerobowam a bakin dāga, a sa jama'ar Isra'ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.’ ”


“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce a kan Ahab ɗan Kolaya, da Zadakiya ɗan Ma'aseya, waɗanda suke yi muku annabcin ƙarya da sunana. Ga shi, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, zai kashe su a kan idonku.


Gama zan tattara dukan al'ummai su yi yaƙi da Urushalima. Za a ci birnin, a washe gidajen. Za a yi wa mata faɗe. Za a kai rabin mutanen birnin bauta, amma za a bar sauran mutanen a cikin birnin.


An yi wa mata faɗe a cikin Sihiyona, Haka kuma aka yi wa budurwai a garuruwan Yahuza.


haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa. Ga shi, ka aika da wasiƙu da sunanka zuwa ga dukan jama'ar da suke a Urushalima, da zuwa ga Zafaniya ɗan Ma'aseya, firist, da kuma ga dukan firistoci, cewa:


Da ɗan daɗewa bayan da annabi Hananiya ya karya karkiyar da take a wuyan annabi Irmiya, sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce


Kai kuma, Fashur, da dukan waɗanda suke a gidanka, za ku tafi bauta a Babila, za ku shiga Babila, a can za ku mutu, a can za a binne ku, kai da abokanka waɗanda ka yi wa annabcin ƙarya.’ ”


Sa'ad da suke cikin halin ƙaƙa naka yi, za a fyaɗa 'ya'yansu ƙasa, su mutu. Za a washe gidajensu, a yi wa matansu faɗe.”


Ya kori mazaunan wurin sa'ad da jama'arsa suka dirkako, Ya rarraba ƙasar ga kabilan Isra'ila, A nan ya ba su izini su zauna a wurin, a cikin alfarwansu.


Mutanen da suka yi wa annabci, za a jefar da su waje a kan titunan Urushalima, a karkashe su da yunwa da takobi, ba wanda zai binne su, da su, da matansu, da 'ya'yansu mata da maza. Zan sa muguntarsu ta koma kansu.


Don haka, ku ne na fari da za a sa su yi ƙaura Bukukuwanku da shagulgulanku za su ƙare.


Ubangiji ya nuna mini wahayi, sai na ga kwandon ɓaure na ci.


Na ga Ubangiji na tsaye a wajen bagade. Ya yi umarni, ya ce, “Bugi ginshiƙan Haikali don shirayi duka yă girgiza. Farfasa su, su fāɗi a kan mutane! Sauran mutane kuwa, Zan kashe su a wurin yaƙi. Ba wanda zai tsere, ko ɗaya.


Ina dai kallon mulkin nan mai zunubi. Zan hallaka su daga duniya, Amma ba zan hallaka dukan jama'ar Yakubu ba.


Ku aske kanku saboda ƙaunatattun 'ya'yanku. Ku yi wa kanku ƙwaƙwal kamar ungulu, Gama 'ya'yanku za su tafi bautar talala.


Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasar da ta fi girma. A can za ka mutu a kusa da karusan da kake fāriya da su. Abin kunya kake a gidan maigidanka!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ