Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Amos 7:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Abin da ya faɗa ke nan, ‘Za a kashe Yerobowam a bakin dāga, a sa jama'ar Isra'ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Gama ga abin da Amos yake cewa, “ ‘Yerobowam zai mutu ta wurin takobi, kuma tabbatacce Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Amos 7:11
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, Sarkin Assuriya ya ci Samariya, ya kwashe Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.


Zan hallakar da wuraren sujada na zuriyar Ishaku. Za a hallakar da tsarkakan wurare na Isra'ila. Zan fāɗa wa zuriyar sarki Yerobowam da yaƙi.”


Maƙiyana suke ta wahalshe ni dukan yini, A kan kowane abu da nake yi, Kullum suna ta tunanin yadda za su cuce ni!


don mun ji shi yana cewa wai wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan, yă kuma sauya al'adun da Musa ya bar mana.”


suka ce, “Wannan ya ce, wai zai iya rushe Haikalin nan na Allah, ya kuma gina shi a cikin kwana uku.”


Don me ka yi annabci da sunan Ubangiji, ka ce wannan Haikali zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kufai, ba mazauna a ciki?” Sai jama'a duk suka taru, suka kewaye Irmiya cikin Haikalin Ubangiji.


Da suka ji dukan maganar, suka dubi juna a firgice, suka ce wa Baruk, “Ai, sai mu faɗa wa sarki wannan magana.”


Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.


Amaziya, firist, na Betel kuwa, ya tafi ya faɗa wa Yerobowam Sarkin Isra'ila, ya ce, “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a cikin jama'ar Isra'ila. Maganganunsa za su hallakar da ƙasar.


Amaziya kuwa ya ce wa Amos, “Kai maƙaryaci ne na ainihi! Koma ƙasar Yahuza ka nemi abin zaman gari, ka yi ta annabcinka a can.


Ku aske kanku saboda ƙaunatattun 'ya'yanku. Ku yi wa kanku ƙwaƙwal kamar ungulu, Gama 'ya'yanku za su tafi bautar talala.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ