Ubangiji ya ce, “Wani birnin Isra'ila ya aika da soja dubu, Ɗari ne kaɗai suka komo, Wani birni kuma ya aika da soja ɗari ne, Amma goma kaɗai suka komo.”
A fara yanyanka su! 'Ya'ya maza na sarkin nan za su mutu saboda zunuban kakanninsu. Daga cikinsu ba wanda zai taɓa mallakar duniya, ko ya cika ta da birane.
Ya faɗa musu darajar wadatarsa, da yawan 'ya'yansa, da yawan matsayin da sarki ya girmama shi da su, da yadda sarki ya ciyar da shi gaba fiye da sarakuna da barorin sarki.
Zan dai bar ɗaya daga zuriyarka da rai, zai yi mini aikin firist, amma zai makance ya fid da zuciya ga kome. Dukan sauran zuriyarka kuwa za su yi mutuwa ƙarfi da yaji.