Ba za a ƙara jin kiɗan masu molo, da mawaƙa, da masu sarewa, da masu bushe-bushe a cikinki ba, Ba kuma za a ƙara ganin mai kowace irin sana'a a cikinki ba, Ba kuma za a ƙara jin niƙa a cikinki ba,
Lalle zaman da kuka yi na dā, irin wanda al'ummai suke son yi, ya isa haka nan, wato zaman fajirci, da mugayen sha'awace-sha'awace, da buguwa, da shashanci, da shaye-shaye, da kuma bautar gumaka, abar ƙyama.
Na tara wa kaina azurfa, da zinariya, daga baitulmalin ƙasashen da nake mulki. Mawaƙa mata da maza suna raira mini waƙa, ina da dukan irin matan da kowane namiji zai so.
dubu huɗu (4,000) su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu (4,000) kuma za su zama masu raira yabbai ga Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda ya yi.
Dawuda ya umarci shugabannin Lawiyawa su sa 'yan'uwansu mawaƙa su riƙa raira waƙa da murna, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, da molaye, da garayu, da kuge masu amon gaske.