Amos 6:10 - Littafi Mai Tsarki10 Sa'ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga ko wane ne da yake ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?” Sai a amsa, “A'a.” Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |