suka i, wa ikon wuta, suka tsere wa kaifin takobi, suna marasa ƙarfi sai suka zama masu ƙarfi, suka yi jaruntaka a wajen yaƙi, suka fatattaka rundunar waɗansu ƙasashe.
Ko da a ce za ku ci dukan rundunar sojojin Kaldiyawa wadda take yaƙi da ku, sauran waɗanda kuka yi wa rauni da suke kwance a alfarwai za su tashi su ƙone birnin da wuta.’ ”
Sai Yehowash ɗan Yehowahaz ya ƙwace daga hannun Ben-hadad, ɗan Hazayel, biranen da Ben-hadad ya ci da yaƙi daga hannun Yehowahaz, tsohonsa. Sau uku Yehowash ya ci shi da yaƙi, sa'an nan ya karɓe biranen Isra'ila.
Ya Urushalima, dukan baƙin da suka auka miki da yaƙi za a hure su kamar yadda iska take hure ƙura, sojojinsu kuma masu firgitarwa za a hure su kamar yadda iska take hure tattaka. Farat ɗaya ba zato ba tsammani,