Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Amos 5:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Ku tafi wurin Ubangiji ku tsira. Idan kuwa kun ƙi, Shi zai babbaka jama'ar Yusufu Kamar yadda a kan babbaka da wuta. Wuta za ta ƙone jama'ar Betel, Ba kuwa mai kashe wutar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ku nemi Ubangiji ku kuma rayu, ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta; zai cinye Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Amos 5:6
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku juyo wurin Ubangiji, ku yi addu'a gare shi, Yanzu da yake kusa.


Ku yi ƙoƙari, ku yi nagarta, ba mugunta ba, Domin ku tsira. Sa'an nan ne Ubangiji Allah Maɗaukaki Zai kasance tare da ku sosai, Kamar yadda kuka ɗauka!


Ubangiji ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Ku zo gare ni, za ku tsira.


Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?’


“Zan sa jama'ar Yahuza ta yi ƙarfi, Zan ceci jama'ar Yusufu. Zan dawo da su domin ina jin tausayinsu. Za su zama kamar waɗanda ban taɓa ƙyale su ba, Gama ni Ubangiji Allahnsu ne, Zan amsa musu.


Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi, Ku shafe jiki da mai mafi kyau, Amma ba ku yin makoki saboda lalacewar Isra'ila.


sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce zan karɓe sandan Yusufu, wanda yake a hannun Ifraimu da mutanen Isra'ila magoyan bayansa, in haɗa shi da sandan Yahuza in maishe su sanda guda a hannuna.


Saboda haka ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Duba, zan kwarara fushina da hasalata a kan wannan wuri, a kan mutum duk da dabba, da akan itatuwan saura da amfanin gona. Zai yi ta cin wuta, ba kuwa za a kashe ba.”


Ya ku mutanen Yahuza da na Urushalima, Ku yi wa kanku kaciya domin Ubangiji, Ku kawar da loɓar zukatanku Don kada fushina ya fito kamar wuta, Ya cinye, ba mai iya kashewa, Saboda mugayen ayyukan da kuka aikata.”


Daidai kamar yadda busasshen itacen da tartsatsin wuta ya fāɗa wa, haka mutane masu iko za su hallaka ta wurin mugayen ayyukansu, ba wanda zai iya hana a hallaka su.


Yerobowam mutum ne mai fasaha. Da Sulemanu ya ga shi saurayi ne mai himma, sai ya shugabantar da shi kan aikin tilas na gidan Yusufu.


Gama na sani, ranka ya daɗe, na yi laifi, shi ya sa na zama na farko daga gidan Yusufu yau da na fito domin in taryi ubangijina sarki.”


Sai su raba ƙasar kashi bakwai. Kabilar Yahuza za ta ci gaba da zama a yankin ƙasarta a wajen kudu, mutanen gidan Yusufu kuwa su zauna a yankin ƙasarsu a wajen arewa.


Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai cinyewa, shi kuma mai kishi ne.


“Idan wuta ta tashi a jeji ta ƙone tarin hatsi, ko hatsin da yake tsaye, ko gona, wanda ya sa wutar lalle ya biya cikakkiyar ramuwa.


Ka ce, “Zo wurina,” Zan kuwa zo gare ka, ya Ubangiji,


“Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni, Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai! Zan yi tabbataccen alkawari da ku, Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.


“Ran da na hukunta mutanen Isra'ila saboda zunubansu, Zan hallakar da bagadan Betel. Za a kakkarya zankayen bagaden, Su fāɗi ƙasa.


Ku nemi Ubangiji, Dukanku masu tawali'u na duniya, Ku waɗanda kuke bin umarninsa. Ku nemi adalci da tawali'u. Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.


Gama fushina ya kama wuta, Tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za ta cinye duniya da dukan amfaninta, Za ta kama tussan duwatsu.


Da yake sun bar bina suka ƙona turare ga gumaka domin su sa ni in yi fushi da dukan ayyukan hannuwansu, saboda haka zan yi fushi da wannan wuri, ba kuwa zan huce ba.’


Ubangiji yana kasa kunne ga masu bukata, Bai manta da jama'arsa da suke a kurkuku ba.


Irmiya kuwa ya ce masa, “Ba za a bashe ka gare su ba. Kai dai ka yi biyayya da maganar Ubangiji wadda nake faɗa maka yanzu. Yin haka zai fi maka amfani, za ka tsira.


Ka faɗa wa ƙasar Isra'ila, ka ce, ni Ubangiji na ce ina gāba da ita. Zan zare takobina daga cikin kubensa, in karkashe adalai da mugaye daga cikinta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ