Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Amos 5:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Kada ku tafi ku yi sujada a Biyer-sheba. Kada ku yi ƙoƙarin nemana a Betel, Gama Betel lalacewa za ta yi. Kada ku tafi Gilgal, Gama an ƙaddara wa jama'arta su yi ƙaura.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 kada ku nemi Betel, kada ku je Gilgal, kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba. Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta, za a kuwa mai da Betel ba kome ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Amos 5:5
34 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ko da yake mutanen Isra'ila suna karuwanci, Kada kuma mutanen Yahuza su yi laifi. Kada ku tafi Gilgal, Ko ku haura zuwa Bet-awen. Kada ku yi rantsuwa da cewa, ‘Har da zatin Ubangiji!’


Waɗanda suka yi rantsuwa da gumakan Samariya, Waɗanda suka ce, ‘Na rantse da gunkin Dan, Da ran gunkin Biyer-sheba,’ Irin waɗannan mutane za su fāɗi, Ba za su ƙara tashi ba.”


Ubangiji ya ce, “Jama'ar Isra'ila, Ku tafi Betel, tsattsarkan wuri, Ku yi ta zunubi! Ku tafi Gilgal ku ƙara zunubi! Ku yi ta kawo dabbobi sadaka kowace safiya. A kowace rana ta uku Ku yi ta ba da zaka.


Ibrahim kuma ya dasa itacen tsamiya a Biyer-sheba, a can ya yi kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami.


Domin a sa'a ɗaya duk ɗumbun dukiyar nan ta hallaka.” Sai duk masu jiragen ruwa, da masu shiga, da masu tuƙi, da duk waɗanda cinikinsu ya gamu da bahar, suka tsaya a can nesa,


Duk da haka dai muna sanar da hikima ga waɗanda suka kammala, sai dai ba hikimar wannan zamani ba, ba kuwa ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda suke shuɗewa ba.


Allah ya zaɓi abin da yake ƙasƙantacce, wulakantacce a duniya, har ma abubuwan da ba su, domin yă shafe abubuwan da suke akwai.


to, ga abin da Ubangiji ya ce maka, ya kai Amaziya, ‘Matarka za ta zama karuwa a birni, za a karkashe 'ya'yanka a cikin yaƙi. Za a rarraba wa waɗansu ƙasarka, kai kanka kuwa za ka mutu a ƙasar arna. Za a sa jama'ar Isra'ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.’ ”


Idan akwai laifi a Gileyad, Hakika za su zama wofi. A Gilgal ana sadaka da bijimai, Bagadansu za su zama kamar tsibin duwatsu A gyaffan kunyoyin gona.”


Za a hallaka masujadan tuddai na Awen inda Isra'ila suke yin zunubi, Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma a bagadansu. Za su ce wa manyan duwatsu, “Ku rufe mu!” Su ce wa tuddai, “Ku faɗo bisa kanmu!”


Ubangiji ya ce, “Kowace irin muguntarsu tana a Gilgal, A can na ƙi su! Saboda mugayen ayyukansu, zan kore su daga ƙasata, Ba kuma zan ƙaunace su ba. Dukan shugabanninsu 'yan tayarwa ne.


Zai zama ƙarshen waɗanda suke zaluntar waɗansu, suna raina Allah. Za a hallakar da kowane mai zunubi.


Ku yi ta shirye-shiryenku! Amma ko kusa ba za ku yi nasara ba. Ku yi magana a kan dukan abin da kuke so! Amma duk a banza, gama Allah yana tare da mu.


Ubangiji yakan sassoke manufofin sauran al'umma, Yakan hana su aikata shirye-shiryensu.


Amma zai sa maƙiyanka su sha kunya, Za a shafe gidajen mugaye.”


Sai Sama'ila ya ce wa jama'a, “Ku zo, mu tafi Gilgal a yi wankan sarautar a can.”


A kowace shekara yakan fita rangadi zuwa Betel, da Gilgal, da Mizfa, inda yakan yi musu shari'a.


Za ku haifi 'ya'ya mata da maza, amma ba za su zama naku ba, gama za a kai su bauta.


Don haka aka kira wannan wuri Biyer-sheba, domin a can ne su duka suka yi rantsuwa.


Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyun kuma Abaija. Su ne alƙalai a cikin Biyer-sheba.


Sai sarki Yerobowam ya yi shawara, ya siffata 'yan maruƙa biyu da zinariya. Sa'an nan ya ce wa jama'arsa, “Zuwanku Urushalima ya isa, yanzu ga allolinku, ya Isra'ilawa, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar.”


Ya kafa siffar maraƙi ɗaya a Betel, ɗayan kuma a Dan.


“Ran da na hukunta mutanen Isra'ila saboda zunubansu, Zan hallakar da bagadan Betel. Za a kakkarya zankayen bagaden, Su fāɗi ƙasa.


Amaziya, firist, na Betel kuwa, ya tafi ya faɗa wa Yerobowam Sarkin Isra'ila, ya ce, “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a cikin jama'ar Isra'ila. Maganganunsa za su hallakar da ƙasar.


Amma a nan Betel kada ka ƙara yin annabci. Nan wurin yin sujada na sarki ne, haikali ne na al'umma.”


Ya sa mata suna Sheba, domin haka har yau sunan birnin Biyer-sheba.


Sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “A wannan rana na kawar muku da zargin Masar.” Saboda haka, har wa yau ake kiran sunan wurin Gilgal, wato a kawar.


Ya fitar da dukan firistoci daga cikin garuruwan Yahuza, sa'an nan ya lalatar da matsafai na kan tuddai inda firistoci suka ƙona turare, tun daga Geba har zuwa Biyer-sheba. Ya kuma rurrushe matsafai na kan tuddai waɗanda suke a ƙofofin shiga ƙofar Joshuwa, hakimin birnin, waɗanda suke hagu da ƙofar birnin.


Sa'an nan Kemosh zai kunyatar da Mowab, kamar yadda Betel wadda Isra'ilawa suka dogara gare ta ta kunyatar da su.


Zan ragargaje ƙyamaren ƙofofin birnin Dimashƙu, In kawar da masu sarautar Bet-eden da na kwarin Awen. Za a kwashe mutanen Suriya ganima zuwa ƙasar Kir.”


Zan hallakar da wuraren sujada na zuriyar Ishaku. Za a hallakar da tsarkakan wurare na Isra'ila. Zan fāɗa wa zuriyar sarki Yerobowam da yaƙi.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ