sai ya fita ya taryi Asa, ya ce masa, “Ka ji ni, ya Asa, kai da dukan Yahuza da Biliyaminu, Ubangiji yana tare da ku idan kuna tare da shi. Idan kuwa kun neme shi, za ku same shi, amma idan kun rabu da shi, shi ma zai rabu da ku.
Ku nemi Ubangiji, Dukanku masu tawali'u na duniya, Ku waɗanda kuke bin umarninsa. Ku nemi adalci da tawali'u. Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.
“Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni, Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai! Zan yi tabbataccen alkawari da ku, Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.
“Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.
Ku tafi wurin Ubangiji ku tsira. Idan kuwa kun ƙi, Shi zai babbaka jama'ar Yusufu Kamar yadda a kan babbaka da wuta. Wuta za ta ƙone jama'ar Betel, Ba kuwa mai kashe wutar.
A shekara ta takwas ta mulkinsa, a lokacin yana yaro, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma, sha biyu, sai ya fara tsarkake Yahuza da Urushalima daga masujadai, da Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da siffofi na zubi.
ya ce musu, “Ku riƙe dukan waɗannan kalmomi a zuciyarku, waɗanda nake yi muku kashedi da su a yau don ku umarci 'ya'yanku su kiyaye dukan maganar dokokin nan sosai.
Waɗanda suka tafi Masar neman taimako, sun shiga uku! Suna dogara ga ƙarfin tulin dawakan Masar na yaƙi, da karusansu, da sojojinsu. Amma ba su dogara ga Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila ba, ba su ko roƙe shi taimako ba.
“Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya, na aikata abin da yake mai kyau a gabanka.” Sai ya yi ta rusa kuka.
Irmiya kuwa ya ce masa, “Ba za a bashe ka gare su ba. Kai dai ka yi biyayya da maganar Ubangiji wadda nake faɗa maka yanzu. Yin haka zai fi maka amfani, za ka tsira.